An kai mace gidan karuwai saboda ta haifi maza

Hakkin mallakar hoto hazel thompson takenebook
Image caption A daya bangaren al'adar kashe 'ya'ya mata ya zama ruwan dare a kasar

'Yan sanda a birnin Calcutta da ke gabashin Indiya sun ce suna binciken zargin da wata mata ta yi cewa surukanta sun kaita gidan karuwai, saboda ba ta haifi 'ya mace ba.

Wata kungiyar agaji da ke ceto karuwai ce ta ceto matar a karshen mako, kafin a kai ga tilasta mata shiga karuwancin.

Matar ta shaida wa BBC cewa 'yan uwan mijinta sun fara cin mutuncinta ne bayan ta haifi 'ya'ya maza uku a jere.

Ana dai zargin cewa al'adar gidan mijin ne su tura 'ya'ya mata karuwanci.