Tsofaffin ministocin Jonathan sun sha kaye

Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Jam'iyyar PDP na fuskantar kalubale daga APC

Wasu daga cikin ministocin da suka ajiye aikinsu a gwamnatin Goodluck Jonathan sun sha kaye a zaben fitar da gwani da aka yi na jam'iyyar PDP a Nigeria.

Tsohon ministan yada labarai, Labaran Maku ya sha kashi a kokarinsa na samun tikitin zama dan takarar gwamna na PDP a jihar Nasarawa.

Can kuma a jihar Ebonyi tsohon ministan lafiya, Farfesa Onyebuchi Chukwu ne ya sha kashi a yayin da tsohon ministan kwadago, Emeka Wogu ya sha kaye a jihar Abia.

A jihar Delta kuwa tsohon ministan Niger Delta, Godsday Orubebe ne ya sha kaye, a yayin da Musiliu Obanikoro ya sha kaye a jihar Lagos a yukunrin samun tikitin zama gwamna a inuwar jam'iyyar PDP.

Kawo yanzu tsohon karamin ministan ilimi, Nyesom Wike ne kadai wanda ya samu nasarar zama dan takarar jam'iyyar PDP a jihar Rivers.

A tsakiyar watan Oktoba ne Mr Jonathan ya sanar da cewa ministocinsa guda bakwai sun ajiye mukamansu domin shiga takarar gwamna a jihohinsu.