'Yan Al-Ka'ida sun saki Serge Lazarevic

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Serge Lazarevic ya shafe shekaru uku a hannun Al Kaida

Kasar Faransa ta ce an sako Serge Lazarevic, ya isa birnin Yamai. Shi ne dai dan kasarta guda da ya rage a hannun kungiyar Al Ka'ida a kasar Mali.

A shekara ta 2011 ne, kungiyar ta Al Ka'ida ta sace shi ta kuma yi garkuwa da shi a Maghreb.

Shugaban Faransa, Francois Hollande ya ce Faransa ba ta da sauran wadanda aka yi garkuwa da su a duk wata kasa a duniya.

Yin garkuwa da mutane ya zama wata hanyar samun kudi a kasashen Mali da sauran kasashen yankin Sahel, amma kuma kasar ta Faransa ta ce ba ta taba biyan kudaden fansa ba.