Ribadu ya ci zabe, Maku ya fadi

Image caption 'Yan takara da dama na ci gaba da yin korafi game da zaben fitar da gwanin

Tsohon shugaban hukumar EFCC a Najeriya malam Nuhu Ribadu na cikin 'yan takarar da suka lashe zaben fitar da gwani domin yi wa jam'iyyar PDP takara a zaben 2015.

Sai dai yayin da Ribadu ya kai bantensa, tsohon ministan watsa labarai, Labaran Maku ya sha kasa a zaben fitar da gwanin da aka gudanar a jiharsa ta Nasarawa.

Ribadu zai fafata da Sanata Bindo Jibrila na jam'iyyar APC a jiharsu ta Adamawa.

Kazalika, tsohon ministan ilimi, Wike Nyesom ya lashe zaben fitar da gwani na PDP a jihar Rivers.

Shi ma tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan kasar, Teslim Folarin ya lashe zaben fitar da gwanin a jiharsa ta Oyo.

A jihohi da dama dai ana ci gaba da yin korafi kan yadda aka gudanar da zaben.