Amazon na fuskantar cikas wajen amfani da jirage maras matuka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Amazon ya sanar da jirgin Prime Air

Kamfanin Amazon ya ce maiyiwuwa zai yi gwajin jirginsa maras matuki a wajen Amurka saboda tsauraran dokokin jirgin maras matuki.

Kamfanin dillacin Labaru na Reuters ya ruwaito cewa tun watan Yuli Kamfanin yake jiran samun amincewar hukumar gudanarwar zirga- zirgar jiragen sama (FAA) domin gwajin jiragensa marasa matuka kusa da Seattle.

Amazon ya sanar da shirinsa na soma amfani da jirgi maras matuki mai suna Amazon Prime Air wajen daukar kaya a watan Disambar shekarar 2013.

Amazon na son amfani da kananan jirage maras matuka ne wajen daukar kaya masu nauyin kilogiram 2.3.

Hakan bai wa kwastomomi damar karbar kayan da suka saya cikin mintina 30 bayan sun yi oda.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Amurka ta amincewa kamfanonin da zasu gudanar da jiragen maras matuka guda shida su yi gwajin jiragensu a kusan lokaci guda, amma kamfanin Amazon ba ya cikinsu.

Wadanda suka sami nasara sun hada da Jami'ar Alaska da filin jirgin sama na Griffiss dake birnin New York da kuma sashen ciniki na arewacin Dakota

Hukumar FAA ta ce tana la'akari ne da abubuwa da suka hada da yanayi da wuri da ababan more rayuwa dake kasa da tsaron lafiya wajen zabar kamfanonin da zasu yi aiki da irin wadannan jirage maras matuka.

Kamfanonin Google da na DHL su ma na duba yiwuwar amfani da jirage maras matuka wajen kai aika sako.