Masu da'awar Jihadi sun kashe mutane 5,000 a Nuwamba

Hare-haren masu da’awar jihadi yayi sanadiyar hallaka mutane fiye da 5,000 a cikin wata guda, kamar yadda binciken da BBC tare da kwalejin Kings na London ya gano.

Fararen hula su ne abin ya fi shafa, inda ‘yan jihadi suka kashe mutane fiye da 2,000 a wasu hare-hare a cikin watan Nuwamba. Kungiyar IS ce ta fi kaddamar da hare-hare, inda ta hallaka mutane da dama a Iraki da Syria. Duba wannan taswirar domin karin bayani

A kasashe hudu aka kashe kashi 80 na adadin mutanen

A kalla mutane 5,042 aka kashe a hare-hare 664 na ‘yan jihadi a kasashe 14, watau kenan a kullum kusan mutane 168 ke mutuwa.

Kashi tamanin cikin dari na kisan an yi ne a kasashe hudu – Iraki da Nigeria da Syria da kuma Afghanistan.

Kasar Iraqi ta fi hadarin zama, inda aka kashe mutane 1,770 a hare-hare 233 ta hanyar harbe-harbe ko kuma harin kunar bakin wake.

A Nigeria , mutane 786 aka kashe, galibinsu fararen hula a hare-haren ‘yan Boko Haram 27. Hanyoyin kisan sun hada da hare-haren da dasa bama-bamai da kuma harbin bindiga. Daga ciki har da wani mummunan hari a babban masallacin Juma’a na Kano inda aka kashe mutane 120.

Boko Haram ta kaddamar da hari a tsallaken iyakar Nigeria da Kamaru inda ta hallaka mutane 15. Haka kuma a gabashin Afrika, Al-Shabab ta kashe mutane 266 a Somalia da kuma Kenya.

An kashe mutane a Afghanistan kusan dai-dai da na Nigeria, inda mutane 782 suka hallaka. Amma hare-haren ba su da girma, kamar harin da aka kai inda aka dabawa mataimakin gwamnan Kandahar wuka.

An kashe mutane 693 a Syria, inda ake fama da yaki, sai kuma Kasar Yemen da ke bi mata baya ga mutuwar mutane 410 a hare-hare 37.

Daga cikin kungiyoyi 16 da ke da hannu a wannan zubda jini, kungiyar IS ce ta fi hadari inda ta kashe mutane 2,206 a Iraki da Syria watau kashi 44 cikin 100 na adadin kisan da aka yi.

Peter Neumann, Farfesa a fannin tsaro a kwalejin Kings ta London, ya ce kungiyar IS “ta maye gurbi ko kuma ta shiga gaban al-Qa’ida a matsayin jagorar jihadi a duniya.”

Fararen hula ne abin ya fi shafa

Fararen hula su ne aka fi kashewa a hare-haren, inda jumlar mutane 2,079 suka mutu, sai kuma jami’an tsaro 1,723.

Amma lamarin ya sha bam-bam sosai a tsakanin kasashe. A Nigeria, an kashe fare-faren hula 700 daga cikinsu 57 yara kanana ne, sai kuma jami’an tsaro 28.

Sai dai kuma a Syria da Afghanistan, adadin sojojin da suka mutu sun linka adadin fararen hula.

Daga cikin ‘yan sanda 146 da suka mutu, 95 a Afghanistan ne.

An kai hari kan ‘yan siyasa da jami’an gwamnati a kasashen Afghanistan da Somalia kuma daga cikinsu an kashe mutane 22.

Bama-bamai da harsasai sun fi kisa

A jumlace, bama-bamai sun janyo mutuwar mutane 1,653, daga ciki 650 ta hanyar kunar bakin wake sannan kuma 555 ta hanyar dasa bama bamai.

Hare hare da bindigogi sun hallaka rayuka akalla 1,574 sannan wasu karin 666 ta hanyar kwanton bauna, inda akasarinsu akwai harbe harbe.

An kashe mutane 426 ciki har da fille kan mutane a kalla 50 a Syria da Yemen da kuma Libya.

Barin wuta ya janyo mutuwar mutane 204 sannan wasu 49 sun mutu sakamakon hari da wukake ko adduna.