Malala ta karbi lambar yabo ta Nobel

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Malala da Satyarthi

Yarinyar nan 'yar kasar Pakistan Malala Yousafzai, da 'yan kungiyar Taliban suka harba shekaru biyu da suka gabata ta karbi lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel a wani biki a Oslo babban birnin kasar Norway.

Malala 'yar shekaru 17 mai fafitikar samun 'yancin ilimin 'yaya mata ta samu lambar yabon tare da wani dan kasar India mai fafitikar 'yancin kananan yara na kasar Kailash Satyarthi.

Yayinda yake magana a bikin, shugaban kwamitin bayar da kyautar Nobel na kasar Norway Thorbjørn Jagland, ya ce duk da cewa Malala na da karamin shekaru, labarinta ya baza duniya.

Ya ce ''Malala Yousafzai ta kasance mai mafi kankantar shekaru da ta samu lambar yabo a wannan zamani amma labarinta ko shakka babu ya baza duniya."