Taron yaki da rashawa a Niger ga 'yan jarida

Shugaba Muhamman Issofou na Nijer Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Muhamman Issofou na Nijer

A Jamhuriyar Nijar, hukumar yaki da cin hanci da rashawa HALCIA ta gudanar da wani taro don fadakar da 'yan jaridu.

Fadakarwar zata karkata ne game da irin rawar da ya kamata su rika takawa don magance matsalar cin hanci da rashawa.

An dai shirya wannan taro ne yayin bikin ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don yaki da cin hanci da rashawa.

'Yan jaridar dake halartar wannan taro sun ce yana da muhimmanci sdaboda irin rawar da suke takawa ta leken sirri. Ta wannan hanya idan aka tsegunta musu wani labari, za su yi bincike su fallasa maganar hukumomi su dauki mataki.

Karin bayani