Ministan Falasdinawa ya rasu a wurin zanga-zanga

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zaid Abu Ein a lokacin zanga-zanga a watan da ya wuce

Ministan harkokin tsaron Isra'ila, Moshe Yaalon,ya bayyana takaici game da mutuwar ministan gwamnatin Palasdinawa Ziad Abu Ein,bayan wani artabu da dakarun Isra'ila.

Mr Yaalon ya ce, ana bincikar lamarin wanda ya faru a yankin gabar yamma ta kogin Jordan dake mamaye.

Wasu hotuna sun nuna wani dansadan kan iyaka na Isra'ila rike da makoshin ministan a lokacin wata zanga-zanga kan dashen itatuwa.

Shugaban Palasdinawa, Mahmud Abbas ya bayyana kisan a matsayin wani abu na dabbanci da ba za a lamunta ba.

Shima sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya ce yana mai matukar bakin ciki kan abinda ya kira kisan rashin imani.