APC: Atiku ya taya Buhari murna

Image caption Atiku Abubakar ya ce nasarar Buhari ta yi daidai

Tsohon mataimakin shugaban Nigeria, Alhaji Atiku Abubakar ya taya Janar Muhammadu Buhari murnar lashe zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC.

A sakon da ya rubuta a shafinsa na Twitter, Atiku ya ce wakilan jam'iyyar sun bayyana matsayinsu kuma Buhari ya cancanci wannan nasarar.

Janar Buhari shi ne zai wakilci jam'iyyar APC a zaben shugaban kasa na 2015.

Buhari ya samu kuri'u 3,430 a yayinda Atiku ya samu kuri'u 954.

Babban kalubalen da ke gaban Janar Buhari shi ne fafatawa tsakaninsa da Shugaba Jonathan na PDP watau kamar maimaicin zaben da aka yi a shekara ta 2011.