'Boko Haram ka iya durkusar da al'amura a Kamaru'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Kamaru na kokarin kare garuruwan da ke bakin iyaka da Najeriya

Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da yankin Afrika ta tsakiya, Abdoulaye Bathily, ya gabatar da rahoto kan halin da wasu yankunan Kamaru masu makwabtaka da Najeriya ke ciki.

Mr. Bathily ya gabatar da rahoton ne a gaban kwamitin tsaro na Majalisar, inda ya ce hare-haren Boko haram na babbar barazana ga durkushewar al'amura a yankin arewacin Kamaru.

Babban jami'in ya kuma yi bayyani kan koma bayan da tattalin arzikin da arewacin Kamaru ke fuskanta sakamakon hare-haren na Boko Haram.

Dubban 'yan Nigeria ne ke gudun hijira a yankin arewa mai nisa na Kamaru sakamakon hare-haren Boko haram a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.