ICC ta bukaci a mika matar Gbagbo

Fatou Ben Souda ta ICC Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fatou Ben Souda ta ICC

Kotun hukunta manyan laifukka ta Duniya, ICC, ta bukaci Ivory Coast ta mika mata uwar gidan tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo, wanda tuni yake jiran shari'a a Hague.

Kasar ta Ivory Coast dai ta ki mika Simone Gbagbo, wacce ake zargi da aikata laifukkan da suka jibinci cin zarafin bil-Adama, tana mai cewa tuni ta kaddamar da bincike a kan mai dakin tsohon shugaban kasar.

Kotun ta kuma tabbatar da tuhume-tuhume har guda hudu a kan abokin huldar Mista Gbagbo na kut-da-kut, Charles Ble Goude.

Ana dai zargin mutanen uku ne da kitsa tashe-tashen hankula a kasar ta Ivory Coast bayan Mista Gbagbo ya ki amincewa da shan kaye a wani zaben shugaban kasa da aka gudanar shekaru hudu da suka wuce.