Amurka ta yi tur da hare-haren Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Amurka ta ce tana hada gwiwa da Najeriya domin kawar da Boko Haram

Gwamnatin Amurka ta yi Allah-wadai da hare-haren da aka kai a Kano da Jos da ke Najeriya.

A wata sanarwa da ofishin jakadancin kasar da ke Abuja ya fitar ranar Juma'a, Amurka ta bayyana hare-haren a matsayin na rashin hankali.

Ta mika ta'aziyyar ta ga 'yan uwan mutanen da lamarin ya shafa.

A cewarta, har yanzu tana hada gwiwa da gwamnatin Najeriya domin kawo karshen hare-haren da 'yan Boko Haram ke kai wa a wasu sassan kasar.