Wanene zai zama mataimakin Buhari?

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Buhari ya ce APC ce za ta zabi mataimakinsa

A Najeriya, bayan zaben da jam'iiyar APC ta yi wa Janar Muhammadu Buhari domin yi mata takarar shugaban kasa a zaben 2015, yanzu hankula sun koma kan wanda zai zama mataimakinsa.

A zaben fitar da gwanin da jam'iyyar ta kammala ranar Alhamis, Janar Buhari ya lashe shi da kuri'a 3,430.

Gwamnan Kano, Rabi'u Kwankwaso ne ya zo na biyu da kuri'u 974, yayin da tsohon mataimakin shugaban kasar, Alhaji Atiku Abubakar ya zo na uku da kuri'u 954.

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya samu 674, yayin da mawallafin jaridar Leadership, Sam Nda Isiah ya samu kuri'u 10.

Jonathan zai tafi da Sambo

Yanzu haka dai 'yan jam'iyyar da ma 'yan Najeriya na bayyana mabambantan ra'ayoyi kan wanda suke gani ya cancanta ya zama mataimakin Janar Buhari.

Sunayen mutane da dama sun fito fili a cikin wadanda ake gani za su iya samun wannan kujerar, cikinsu har da gwamnan Legas, Babatunde Fashola da na Rivers Rotimi Amaechi da na Edo, Adams Oshimhole da dai sauransu.

Sai dai a wata hira da wata kafar watsa labaran Najeriya ta yi da Janar Buhari a makon jiya, ya ce jam'iyyarsa ce kawai za ta zabi wanda zai zama mataimakinsa.

Shi dai shugaba Goodluck Jonathan wanda zai yi wa jam'iyyar PDP takarar shugaban kasa, ya zabi Arch. Namadi Sambo a matsayin mataimakinsa.