2015: Jonathan da Buhari za su ja-zare

Hakkin mallakar hoto AFP AP
Image caption Masu sharhi sun ce zaben 2015 zai yi zafi

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan zai kara fafatawa da tsohon shugaban mulkin soja, Janar Muhammadu Buhari a zaben da za a gudanar a shekara ta 2015.

Mr Jonathan shi ne wanda jam'iyyar PDP ta bai wa tikitin zama dan takararta a yayin da Janar Buhari zai daga tutar jam'iyyar APC mai adawa a zaben.

Zaben shugaban kasa na 2015 a Nigeria zai kasance tamkar maimacin zaben da aka yi ne a 2011, inda Mr Jonathan ya kara da Janar Buharin amma ya samu nasarar doke shi a wancan lokacin.

Mr Jonathan na neman ta-zarce ne a karo na biyu a yayin da Janar Buhari ke takara a karo na hudu, bayan rashin nasararsa a 2003 da 2007 da kuma 2011.

Masu sharhi na ganin cewar zaben na badi zai yi zafi sosai kasancewar 'yan adawa sun dunkulle waje guda a yayinda jam'iyyar PDP mai mulki ke shan suka kan yadda take gudanar da mulkin kasar.

Jam'iyyar PDP ce ke mulkin Nigeria tun daga shekarar 1999 da kasar ta koma bin tafarkin mulkin demokradiyya.

'Yan adawa na zargin gwamnatin Jonathan da kasa yin abin da ya dace domin murkushe ayyukan 'yan Boko Haram wadanda suka kashe dubban mutane da kuma raba mutane fiye da miliyon daya da muhallansu.