CIA ta kare matakan ganawa mutane ukuba

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mr. Brennan ya ce hanyoyin tatsar bayanai na "musanman" su suka sa aka gano inda Osama Bin Laden ya buya

Daraktan hukumar leken asiri ta kasar Amurka-CIA, Mr. John Brennan ya sake kare hukumar sakamakon zarginta da ganawa 'yan kungiyar Al'qaeda ukuba don tatsar bayanai, ba tare da an samu sakamako ba.

Mr. Brennan ya ce yana da wahala jama'a su iya gane ko hanyoyin tatsar bayanan na "musanman" da hukumar ta yi amfani da su, sun sa an samu muhimman bayanai daga wurin wadanda ake tsare dasu.

Ya ce hukumar ta dauki matakai da dama da suka dace, bayan hare-haren 11 ga watan Satumba, a lokacin da ake ta neman mafita.

Mr. Brennan ya ce bayanan da hukumar ta samu ta hanyar shakawa mutane ruwa da karfin tsiya da kuma hana su barci, sun taimaka wajen tseratar da rayukan Amurkawa tare da ganin bayan Osama Bn Laden.

Sai dai shugabar kwamitin majalisar dattijan daya yi zargin, Senata Dienne Feinstein ta sake kalubalentar hujjojin da Mr Brennan ya bayar.