Facebook zai fara tantance hotuna

Image caption Wasu suna aikawa da hotuna marasa mutunci ta shafin Facebook

Shafin Facebook yana kokarin bullo da wata manhaja ta hana mutane aikawa da hotuna marasa mutunci ta shafin.

Manhajar wadda zata kunshi wani bangare na gane hoto da wasu tambayoyi na dabara, zata iya banbance hotuna masu mutunci dana wadanda ke cikin maye.

Manhajar zata rika tambayar mutane: "ko zaka so mai gidanka ko mahaifiyarka ta ga hoton da kake shirin aikawa?"

Shugaban sashin binciken fasahar dabaru na Facebook, Yann LeCun ne ya sanar da sabon tsarin ga wata mujalla.

Mr. LeCun ya ce nan gaba, sabon tsarin zai iya taimakawa wajen gane mutanen da suke sanya hotunan wasu mutane a shafukansu batare da izinin masu hotunan ba.

Tuni dama shafin Facebook ya ke amfani da wata fasaha ta gane fuskokin mutane, wadda take bai wa masu amfani damar bibiyan mutanen da suke so.

Acewar Mr. LeCun, shafin Facebook ya dade yana amfani da fasahar Artificial Intelligence-AI wajen tantance labaran da suka dace a shafukan jama'a.