Matsalar na'ura a filayen jiragen sama na Birtaniya

Image caption Ana saran warware matsalar daga nan zuwa maraicen ranar Juma'a

Fasinjoji na fuskantar tsaiko a wasu filayen jiragen sama da ke London bayan an samu matsalar na'ura a cibiyar da ke kula da tashi da saukar jiragen sama a Birtaniya.

Hukumomi sun ce matsala ce ta faru a cibiyar Swanwick ta Hampshire abinda ya sa aka taikata zirga-zirga a sararin samaniyar Birtaniya.

Hukumomi sun kara da cewa akwai yiwuyar za a warware matsalar nan bada jimawa ba.

Filin jirgin sama na Heathrow ya bada rahoton cewa ana samun jinkiri a tashi da saukar jiragen sama, a yayinda filin jirgin sama na Gatwick ya ce an dakatar da duka jiragen sama daga tashi.

Sai dai wasu filayen jiragen saman sun ce matsalar ba ta da yawa.