Google zai dauke injiniyoyinsa daga Rasha

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kamfanin Google ya sha sauya wa ma'aikatansa kasashen aiki

Katafaren kamfanin fasaha na Google ya tabbatar da rahotannin da ke cewa yana shirin fitar da injiniyoyinsa daga ofishinsa a Rasha.

Kamfanin ya jaddada kudurinsa na cigaba da biyan bukatun masu amfani da Google a Rasha.

Kamfanin ya shaida wa BBC cewa ya sha sauya wa injiniyoyinsa kasashen aiki a wasu lokuta a baya.

Sai dai kamfanin bai sanarda ko ma'aikata nawa ne za a fidda su daga kasar Rashan ba.

A watan Yuli, majalisar dokokin Rasha ta amince da wata doka da ta bukaci kamfanonin intanet su rika ajiye bayanan da suka shafi jama'ar Rasha a cikin kasar.

Gwamnatin Kremlin ta ce an kafa dokar ce domin kare bayanan jama'a, amma masu adawa suna kallon dokar a matsayin wani yunkuri na sanya takunkumi a harkokin intanet.

Dokar dai zata bai wa gwamnati ikon rufe shafukan intanet da suka ki bin sharuddanta.

Kamfanonin fasahar intanet da yawa suna ajiye bayanan mutane ne a rumbunan adana bayanan intanet a fadin duniya, kuma ba sa la'akari da wurin da masu bayanan ke zama.

Mujallar Wall Street Journal ta ce wasu daga cikin ma'aikatan Google kamar msu kula da sha'anin kasuwanci zasu cigaba da aiki a ofishinsa na Rasha.