ICC zata dakatar da binciken Al-Bashir

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Omar Al-Bashir ya kwashe shekaru 25 yana mulki a Sudan

Babbar jami'a mai gabatar da kara a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya-ICC ta ce zata tsayar da binciken zargin aikata laifukan yaki a yankin Darfur na kasar Sudan, saboda rashin samun goyon baya daga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

Fatou Bensouda, ta ce gazawar kwamitin na daukar mataki ya kara karfafa gwiwar masu tafka ta'asa ci gaba da ta'asarsu, musanman ga mata da 'yanmata.

Tun a cikin shekarar 2009 ne kotun ta ICC ta tuhumi shugaba Omar Al-bashir, amma har yanzu ba'a kama shi ba, ko kuma sauran mutane ukun da ake tuhumar su tare.

Mrs Bensouda ta ce yanayin rashin zaman lafiya a Darfur yana kara kazancewa, yayin da ake cigaba da tafka ta'asa, amma har yanzu babu wani mataki da kwamitin tsaron ya dauka.

Alkaluman Majalisar Dinkin Duniyan sun nuna cewa akalla mutane dubu 300 ne aka kashe a Darfur, yayin da aka tilastawa miliyan 2 barin gidajensu.