Zanga-zanga a kasar Italiya

Dubban Italiyawa sun kwarar kan tituna a wani bangare na wani yajin aikin gama-gari da aka kira don nuna adawa da sauye-sauyen da gwamnati ke shirin yi ga dokokin kwadago na kasar.

Ana gudanar da tarukan gangami a daukacin manyan biranen kasar.

A Turin da Milan ma har an samu 'yar hatsaniya tsakanin 'yan sanda da wasu daga cikin masu zanga-zangar.

Yajin aikin ya kuma kai ga rufe makarantu da asibitoci, ya kuma kawo cikas ga harkokin sufuri a fadin kasar.

'Yan kwadago a kasar dai sun kafa hujja da cewa sauye-saueyn ka iya yin barazana ga ayyuka ta hanyar saukaka korar ma'aikata.

Sai dai FM Matteo Renzi yana ganin cewa wajibi ne a sassauta dokokin kwadago in har ana so masu diban ma'aikata su iya biyan bukatun tattalin arzikin kasar.