Jos: 'Yan kunar bakin wake sun halaka mutane 30

Image caption Yankin arewacin Nigeria na fuskantar munanan hare hare a baya bayan nan

Hukumomin tsaro a Nijeriya sun bayyana cewa ‘yan kunar bakin wake ne suka kaddamar da hare-haren nan na yammacin ranar Alhamis a birnin Jos dake tsakiyar kasar.

Hare-haren a yankin Terminus inda ake hada-hadar kasuwanci dai, sun yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 30, a cewar shaidu da kuma jami’an gwamnati.

Tagwayen hare-haren bama-baman na birnin Jos na zuwa ne bayan wasu hare-hare a masallaci da kuma wata kasuwa a birnin Kano na arewacin kasar a cikin kwanakin nan inda mutane fiye da 100 suka rasa rayukansu.

Yankin arewacin Nigeria na fuskantar munanan hare hare a baya bayan nan.