'An yi amfani da kudi a zabubbuka a Nijeriya'

Hakkin mallakar hoto Getty

A Najeriya a yayin da jam'iyyun kasar suka zabi mutanen da za su tsaya masu takara a matsayin mukaman gwamnoni da 'yan majalisun jaha da na kasa , wasu 'yan siyasar kasar na nuna damuwa game da yadda su ka ce aka yi amfani da kudade a yayin irin wadannan zabubbuka.

Wasu 'yan siyasar Nigeriar dai na cewa babu shakka a zaben fitar da gwanayen da suka gabata musamman a jihohi an fuskanci wannan matsala, don haka su ke fatan ganin an magance irin wannan dabi'a a siyasar kasar don gudun zaben tumin dare.

Malam Nasiru El Rufai dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar APC a jihar Kaduna na ganin cewa 'babu shakka an yi amfani da kudi a zabubukan da aka yi , kuma ba abu bane da zai iya gyaruwa a rana daya ba , sai a hankali' a cewarsa.

Ya kara da cewa jam'iyyar APC na ci gaba da wayar da kan jama'a cewa ba abu bane mai kyau.

Shi kuwa Alhaji Ibrahim Wusono mataimakin shugaban jam'iyyar PDP a Kaduna cewa ya yi amfani da kudi matsala ce ta dukkanin jam'iyyu.

Sai dai ya ce jam'iyyar PDP ta maida hankali ne wajen zabar mutane nagartattu .