Abba ya gargadi 'yan sanda kan yajin aiki

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police
Image caption Sulaiman Abba ya ce zai hukunta duk dan sandan da ya tayar-da-zaune-tsaye

Babban Sifeton 'yan sanda Najeriya, Suleiman Abba ya gargadi jami'an rundunar da su guji yin duk abin da zai tayar da zaune tsaye.

Babban Sifeton 'yan sandan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da rundunar ta fitar, bayan da rahotanni suka ambato wasu 'yan sandan kasar na shirin shiga yajin aiki.

A cewarsa, duk dan sanda da aka kama yana yin kalaman da za su kawo tashin hankali zai yabawa aya zakinta.

'Yan sandan dai na korafi ne saboda rashin biyansu hakkokinsu.

Sulaiman Abba ya kara da cewa yana bin duk hanyar da ta kamata domin ganin an kyautata tsarin ayyukan 'yan sandan kasar.