Shagari: Dole ne a bani takara a PDP

Image caption Zaben fitar da gwani a jam'iyyar PDP a jihohi da dama ya bar baya da kura

Cece-kucen da ya biyo bayan zaben fitar da dan takatar gwamnan jihar Sakkwato a inuwar jam'iyyar PDP ya dauki wani sabon salo.

Mataimakin gwamnan jihar Mukhtari Shehu Shagari wanda ya sha kaye a zaben, ya ce dole ne sai jam'iyyar ta karbe tikitin takarar daga wanda ya lashe, ta kuma ba shi, bisa wata yarjejeniyar da aka yi a baya.

Mataimakin gwamnan dai shi ne ya lashe zaben fitar da gwanin dan takarar gwamnan a shekara ta 2006, amma sai shugaban kasa na wancan lokacin Olusegun Obasanjo ya tilasta masa mika tikitin ga gwamnan jihar na yanzu.

Alhaji Muktari Shagari ya ce a wancan lokacin jam'iyyar ta PDP ta yi masa alkawarin ba shi tikitin kai tsaye idan Gwamna Wamakko ya gama mulki.

Sai dai jam'iyyar PDP reshen jihar sokkoto ta ce su dai sun bi umarnin uwar jam'iyya na gudanar da zaben fitar da gwani, kuma sun yi.