Masar: Za a gurfanar da 439 a kotun soji

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Kimanin mutane 700 ne aka kashe a tashe-tashen hankula bayan hambarar da Mohamed Morsi

A kasar Masar, mutane 439 da ke goyon bayan hambararren shugaban kasar Mohammed Morsi zasu fuskanci shara'a a kotun sojoji bisa zargin tashe-tashen hankula a awatan Agustan bara.

Hakan ya biyo bayan wata doka ce da shugaba Abdel Fattah Al-Sisi ya zartar, wacce ta bada damar a gurfanar da fararen hula da ake zargi da kai hare-hare kan dukiyar gwamnati, a gaban kotunan soji.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi Allah wadai da matakin gurfanar da fararen hula a gaban kotuna soji, inda suka ce babu adalci a kotunan.

Kawo yanzu dai, fiye da magoya bayan hambararren shugaba Morsi dubu 15 ne ke daure a gidajen yari a kasar tun bayan da aka hambarar da shi a watan Yulin bara.

Wasu daruruwa daga cikinsu, hukuncin kisa aka yanke musu.