ICC za ta dakatar da bincike kan Dafur

Babbar mai gabatar da kara ta kotun kasa-kasa Fatou Bensouda ta ce za ta dakatar da binciken manyan laifuka da kotun ke yi a yankin Darfur na Sudan, saboda rashin taimako daga kwamitin sulhu na Majalisar dinkin duniya.

A shekarar 2009 ne Kotu ta zargi Shugaban Sudan din Umar Hassan Al-bashir da kisan-kare-dangi a Darfur.

Sai dai har yanzu ba a kama shi ko daya daga cikin manyan jami'an gwamnatinsa ba.

A wani jawabin da ta yi wa kwamitin, Fatou Bensouda ta ce gazawar Kwamitin sulhun ta sa wadanda ake tuhuma da cin zarafin bil'dama na cigaba da yin abin da suka ga dama.

Fatou Bensouda ta bayyana cewa yanzu za ta yi amfani da dan abin da ke hannun kotun wajen bin kadin zarge-zargen da ake da tabbas a kan su.