Shugaban Sudan ya ce ICC ta ji Kunya

Shugaban Sudan Omar Hassan Al-Bashir Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Sudan Omar Hassan Al-Bashir

Shugaban Sudan Omar Hassan Al-bashir ya yi ikirarin samun nasara akan kotun hukunta muggan laifuka ta duniya, ICC bayan da shugabar kotun Fatou Bensouda ta dakatar da binciken da ake yi a kan sa na zargin aikata laifukan yaki a yankin Darfur.

Shugaban, wanda ake tuhuma da laifuka daban-daban tun shekarar 2009, ya ce kotun ta ji kunya a aniyar ta, ta kunyata kasar sa.

Yace jama'ar Sudan ta kudiri aniyar cewa babu wani dan kasar da zai mika wuya ga duk wata kotun masu mulkin mallaka.

A jiya Juma'a ne Fatou Bensouda ta ce rashin wani katabus daga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na kara wa masu aikata laifukan yaki kwarin gwiwa musamman ma wadanda ke cin zarafin mata.