Za a sake zaben Kakakin majalisar Nijar

Niger
Image caption A mako mai zuwa ake sa ran za a sake zaben

A Jamhuriyar Nijar bangaren masu rinjaye a majalisar dokokin kasar ya ce za a sake zaben sabon shugaban majalisar a farkon mako mai zuwa.

Hakan ya biyo bayan wani hukunci da kotun tsarin mulkin kasar ta yanke a jiya, inda ta ce, ba za ta iya ayyana zaben da aka yi wa Hon. Amadu Salifu a matsayin sabon shugaban majalisar ya yi ko bai yi ba.

Zaben da 'yan adawa suka kauracewa domin ikrarin da suka yi na cewa ba a yi bisa ka'ida ba.

A ranar 4 ga watan Disamba ne wasu 'yan majalisa suka shigar da kara gaban kotun tsarin mulkin kasar domin ta soke zaben na Amadu Salifu.