Boko Haram na horar da matasan Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kamaru na fuskantar Boko Haram a yankunanta na arewa mai nisa da ke kusa da Nigeria

Gwamnatin Kamaru ta ce kungiyar Boko Haram na daukar matasa 'yan kasar marasa aikin yi tana ba su horo a kan akidojinta.

Kakakin gwamnatin Kamaru, Minista Issa Tchiroma Bakary ne ya bayyana haka, inda ya kara da cewa gwamnati ta aika sojoji kusan 6000 domin su tunkari mayakan kungiyar a yankin arewacin Kasar.

Haka kuma Ministan ya ce mayakan Boko Haram sun kai hari kan wani kauye a arewacin kasar (Kangeleri, a karamar hukumar Waza), kuma a yayin harin sun kashe mutane biyu.

Sanarwar ofishin Ministan ta kara da cewa dakarun Kamaru sun kashe 'yan Boko Haram bakwai tare da kama wasu 25, a yankunan arewacin kasar da ke kusa da Najeriya.

Wasu mayakan na Boko Haram din kuma ruwa ya ci su yayin da suke kokarin tserewa, sannan kuma an kwace makamai a wurinsu kamar yadda sanarwar ta bayyana.