Mataimakin Buhari zai fito daga kudu-maso-yamma

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan takarar APC a zaben 2015

Jiga-jigan jam'iyyar adawa ta APC a Nigeria za su yi taro a Abuja babban birnin kasar domin cimma matsaya a kan wanda zai zama dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben shekara ta 2015.

Tun bayan da Janar Muhammadu Buhari ya lashe zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC a ranar Alhamis da ta wuce, kusoshin jam'iyyar suke ta mahawara a kan wanda ya fi caccanta ya zama mataimakinsa.

Wani makusancin Janar Buhari, Alhaji Faruk Adamu Aliyu ya tabbatar wa da BBC cewa ana saran cimma yarjejeniyar samun dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC a taron na ranar Litinin a Abuja.

Bayanai sun nuna cewar daga shiyyar kudu maso yammacin kasar ake saran zaban mataimakin Janar Buhari.

Daga cikin wadanda rahotanni suka ce ana nazari a kan su, sun hada da, gwamnan Lagos Babatunde Fashola da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi da tsohon kwamishinan shari'a na jihar Lagos Farfesa Yemi Osibajo.

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba