An sauya hukunci bayan shekaru 18 da kashe mace

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An yanke hukuncin kisan matar ne a lokacin kamfe din adawa da manyan laifuka

A wani abin da ba a saba gani ba, wata kotu a kasar China ta sauya hukuncin wata shari'a bayan shekaru 18 da kashe matar da aka samu da laifi.

An zartar da hukuncin kisan ne kan matashiyar, mai suna Huugjilt kan shari'ar fyade da kisan kai.

Sai dai bayan an sake fara shari'ar ne kuma wani mutum ya amsa cewa shi ne ya kashe matar da aka samu Huugjilt da laifi.

Iyayen matashiyar sun barke da kuka a yayin da Alkali a Inner Mongolia ya russuna domin mika musu sabon hukuncin.