Kyamar masu auren jinsi daya na karuwa

Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Ana kara kyamar masu auren jinsi daya a Rasha

Kungiyar kare hakkin dan adam Human Rights Watch, ta ce kyamar masu auren jinsi daya na karuwa a kasar Rasha tun lokacin da aka amince da dokar da ta hana yin auren a shekarar da ta wuce.

Kungiyar ta ce ana yawan kai wa masu auren jinsi dayan hari a kasar ta Rasha.

Wani sabon rahoto da kungiyar ta fitar, ya bayyana kyamar da ake yi wa masu auren jinsi daya a matsayin wani lasisi da ke bayar da dama ga jama'a su kai musu hari da kuma daukarsu a matsayin 'yan bora.

Human Rights Watch ta ce hukumomin Rasha suna da ikon hana cin zarafin masu auren jinsi daya, amma sun ki daukar mataki.