An yi garkuwa da mutane a Sydney

Wadanda aka yi garkuwa da su a Sydney Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wadanda aka yi garkuwa da su a Sydney

Daruruwan 'yan sanda dauke da manyan makamai sun killace wasu sassa na tsakiyar birnin Sydney wurinda wani ko wasu masu dauke da bindigogi ya yi garkuwa da wasu mutane a wani gidan shan-shayi.

Ana ganin mutane tsai-tsaye sun dora hannuwansu a kan tagogi wurinda aka sanya wata bakar tuta ta musulunci.

Wani mai magana da yawun 'yan sanda ya ce suna kokarin tuntubar mutanen da aka rutsa da su a ciki. A wani jawabi ta talabijin ga al'ummar kasar Prime Ministan Australia Tony Abbott ya ce, ba a rigaya aka san dalilan garkuwar da aka yi da mutane ba - to amma akwai alamun cewar batun yana da nasaba da siyasa.

Karin bayani