An kubutar da mutane a Sydney

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan sanda sun kubutar da mutane a wurin

Dakarun tsaro a Australia sun kutsa cikin shagon shayin da wani dan asalin kasar Iran ya yi garkuwa da mutane.

An ji kara mai karfin gaske kafin wadanda aka yi garkuwa da su, su tsere daga bisa ni kuma an ji karar harbi babu kakkautawa.

Wasu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su din suna karbar magani a asibiti.

Dan bindigar, Man Haron Monis mai shekaru 49, dan gudun hijira ne daga Iran kuma an bada belinsa ne bayan aika ta wasu manyan laifuka.

An same shi da laifin aika sakwannin batanci ga iyayen sojojin Australia wadanda suka mutu a wurin yaki a kasashen waje.