APC: Osibanjo ya zama mataimakin Buhari

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan takarar shugabancin Nigeria na jam'iyyar APC a 2015 Muhammadu Buhari

Babbar jamiyyar adawa a Nigeria, APC, ta zabi Farfesa Yomi Osibanjo a matsayin mataimakin Janar Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasar da za a yi a watan Fabrairu.

Wani jigo a jam'iyyar kuma makusancin Buhari, Faruk Adamu Aliyu ya shaida wa BBC cewa an cimma wannan matsaya ce bayan taron da jiga-jigan jam'iyyar suka yi da Buharin, bayan sun kasa fitar da mataimakin a ranar Talata.

A hukumance har yazu dai jam'iyyar ba ta annaya wanda zai zama mataimakin Janar Buhari ba.

Farfesa Osibanjo dan kabilar Yarabawa ne kuma kirista daga yankin kudu maso yammacin kasar.

Rahotanni sun ce tun da farko maganar, batun kabilanci da kuma addinin wanda zai kasance mataimakin Janar Buharin ya kawo jinkiri wajen cimma matsaya.