APC ta kasa cimma matsaya kan mataimakin Buhari

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption APC ta amince Buhari ya zabi mataimakinsa

Jiga-jigan jam'iyyar APC a Najeriya sun gaza cimma matsaya a taron da suka yi ranar Litinin domin zaben mutumin da zai zama mataimakin Janar Muhammadu Buhari.

Wata majiya a jam'iyyar ta shaidawa BBC cewa an kasa cimma matsaya ne saboda ra'ayoyin bangarori da dama sun bambanta game da wanda za a tsayar dan takarar mataimakin shugaban kasar.

BBC ta fahimci cewa jami'an jam'iyyar ta APC daga kudu maso yammacin kasar suna so ne a bai wa tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu a matsayin.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Sai dai wasu 'yan jam'iyyar na gani hakan bai kamata ba saboda shi ma musulmi ne kamar Janar Buhari.

Wasu kuma, a cewar majiyar tamu, suna so ne a ba da matsayin ga yankin kudu maso kudancin kasar inda shugaba Goodluck Jonathan ya fito.

Yanzu haka dai rahotanni na cewa an bai wa Janar Buhari ya zabi mataimakinsa da kansa, sabanin kalaman da ya yi a baya cewa jam'iyar ce za ta fitar da mataimakin nasa.

A gobe Laraba ne dai wa'adin da hukumar zaben kasar ta ware domin jam'iyyu su mika mata jerin 'yan takararsu ke karewa.