Facebook zai kare sanya hotunan da ba a so

Kamfanin Sada zumunta na Facebook Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kamfanin Sada zumunta na Facebook

Kamfanin Sada zumunta na Facebook ya bullo da hanyar kawo karsahen tura hotuna maras sa kyau na mutane a Internet.

Kamfanin Sada zumunta na Facebook yana aiki kan wata manhaja wadda za ta kare mutum daga tura hotuna maras sa kyau wadanda ba su so a shafin Internet.

Wannan tsari da kamfanin zai bullo da shi zai iya tantancewa tsakanin hotuna maras sa kyawon gani ko dai na mutanen da suka yi tatil da barasa ko kuma suke cikin wani yanayi maras dadi.

Tsarin, zai tambayi mutum "lallai kana bukatar Oganka da Mamar ka su ga wadannan hotunan ?"

Shugaban Sashen bincike ne na wasu abubuwa na jabu ya bayyana haka ga wata Mujalla.

Yann LeCun yace, yana son bullo da wani tsari ne da zai rinka taimaka ma masu tura abubuwa ta Facebook.

Nan gaba yace, wannan tsarin zai kuma iya taimakawa wajen gane idan wani ya dora hoton wani a shafin na facebook, ba tare da amincewa ko kuma sanin sa ba.

Kamfanin sada zumuntar na Facebook dama yana da wata fasahar ta gane fuskoki tare da baiwa masu shiga shafin dora hotunan daidai.

A yanzu, kamfanin yana kokarin inganta wannan fasahar da manhajar da yake kokarin bullo da ita.

Karin bayani