Ghana na binciken mai fafutuka kan cutar HIV

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cutar HIV ce ta kashe saurayin Joyce, kuma tana shan magungunan yaki da cutar

Hukumar yaki da cutar HIV/AIDS ko SIDA a Ghana da ta kiwon lafiya sun fara wani bincike kan matsayin wata mai wakiltar masu cutar HIV a kasar.

Binciken dai zai tantance ikirarin da Joyce Didjo, ta yi na cewa ba ta dauke da kwayar cutar HIV.

Joyce ta dade tana fafutukar kare hakkin masu dauke da cutar ta HIV/AIDS kafin ta fito a wata kafar yada labarai ta kasar a ranar Litinin ta ce ba ta dauke da kwayar cutar.

Mai fafutukar ta sha tafiye-tafiye kasashen waje a matsayin mai dauke da kwayar cutar HIV da ke wa hukumar kamfe.