Kisan 'yan jarida ya ragu a duniya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kungiyar ta ce satar 'yan jarida ta karu a bana

Wata kungiyar da ke fatutikar kare 'yan jarida a duniya ta ce adadin manema labaran da ake kashewa ya ragu a bana.

Sai dai kungiyar ta Reporters without Borders ta ce 'yan jarida na fuskantar kisa saboda farfagandar da suke watsawa.

A rahoton da ta fitar na shekara, kungiyar ya ce kisan da kungiyar IS ta yi wa wasu 'yan jarida a Syria a wannan shekarar ya nuna cewa "yanzu ana yin kisan ne irin na dabbanci kuma da gangan".

Rahoton ya ce kodayake kisan da ake yi wa 'yan jarida ya ragu da kimanin kashi bakwai cikin dari idan aka kwatanta da bara, amma satar 'yan jarida ta karu da fiye da kashi uku cikin daro.

A cewar rahoton, an fi gallazawa 'yan jarida a yankin Gabas ta tsakiya da Africa.