Ta'addanci: Kenya ta soke rajistar kungiyoyi 500

Image caption Kungiyar Al-Shabbab ta Somalia na ci gaba da kai hare-hare a Kenya

Gwamnatin Kenya ta soke rajistar kungiyoyi fiye da 500 masu zaman kansu a kasar.

Gwamnatin dai ta zargi 15 daga cikin kungiyoyin cewa suna da hannu cikin ayyukan ta'addanci.

Ta kuma rufe asusun bankunansu tare da kwace takardar shaidar aiki na ma'aikatansun da ba 'yan kasar ba.

Haka kuma rahotanni sun ce hukuncin ya biyo bayan wata zazzafar muhawara kan sabuwar dokar tsaro wadda za ta taimaka wajen yaki da ta'addanci.