Kungiyar musulmi ta gargadi 'yan siyasar Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou

Babbar kungiyar musulunci ta Nijar, AIN, ta yi kira ga 'yan siyasar kasar su yi hattara dangane da wasu munanan kalamai da dabi'un da suke nunawa.

Kungiyar na damuwa ne kan yadda ta ce ta lura mahawara kan yi zafi tsakanin 'yan siyasar, har su kai ga furta kalamai na batanci da za su iya raba kan 'yan kasa.

'Yan adawa dai sun dora laifin abin da ke faruwa ga masu ruke da mulki, zargin da su kuma suka musunta.

Hadaddiyar kungiyar Musulman, ta ce kace-nace tsakanin jama'a abu ne da ba za a iya kauce wa ba, amma ya kamata a bar wuce iyaka.