'Mutane miliyan daya ba za su yi zabe a Nigeria ba'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Majalisar Dattawa za ta tattauna batun garonbawul kan dokar zaben

Hukumar zabe ta Nigeria ta nuna fargabar cewa akwai yiwuwar mutane fiye da miliyan daya da suka rasa matsugunansu ba za su yi zabe ba a shekarar 2015.

Inda ta kara da cewa wadanda abin ya shafa za su samu yin zaben ne kawai idan an sauya kundin zaben kasar.

Kundin zaben Najeriya dai ya ce mutum zai kada kuri'a ne kadai a mazabarsa inda ya yi rajista.

Rikicin Boko Haram ya daidaita dubban mutane musamman a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.