Nigeria: Kasuwar 'yan bumburutu ta bude

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu sayar da mai a bayan fage sun koma kan titunan Najeriya

A Najeriya, masu sayar da fetur a bayan fage sun komo kan titunan kasar bayan ma'aikatan man fetur da isakar gas sun fara yajin aiki.

Yanzu haka dai a biranen kasar da dama, ana sayar da man fetur a sama da farashin da aka kayyade sakamakon dogayen layukan man a gidajen sayar da man.

Masu sana'ar sayar da man a bayan fagge, wadanda aka fi sani da 'yan bunburutu na cin karensu babu babbaka, inda suka sayar da man a farashi mai dan karen tsada.

Najeriya dai ita ce kasa ta shida cikin kasashen da ke da arzikin man fetur, amma 'yan kasar na fama da matsanancin talauci.

A shekarar 2012 shugaban kasar Goodluck Jonathan ya kara farashin man fetur, lamarin da ya janyo zanga-zanga a kasar.