Pakistan na zaman makoki na kwana uku

Makarantar da aka kai hari a Pakistan Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Makarantar da aka kai hari a Pakistan

Kasar Pakistan tana zaman makoki na kasa na kwanaki uku sakamakon harin da 'yan Taliban suka kai kan wata Makaranta inda aka kashe mutane fiye da dari da arba'in kusan ma dukkansu kananan yara ne.

An yi jana'izar su a birnin Peshawar an kuma kunna kyandira na juyayi a kusan dukkan biranen kasar.

Babban hafsan hafsoshin sojin kasar ya yi alkawarin ramuwar gayya ga dukkan wani jinin da aka zubar lokacin hare-haren da aka kai a ranar Talata.

Kungiyar Taliban ta Afghanistan mai alaka ta kut-da-kut da kungiyar Taliban ta Pakistan, ta yi tur da harin da aka kai kan Makarantar dake Peshawar, tana mai cewa kisan Mata da Kananan Yara abu ne da ya saba ma addinin Musulunci.

Karin bayani