'Yan Taliban sun kashe mutane 141 a Pakistan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun Pakistan sun killace yankin

Mayakan Taliban sun kai hari kan wata makaranta a yankin Peshawar na Pakistan, inda suka hallaka mutane kusan 141.

Ministan lardin, Khyber Pakhtunkhwa ya ce daga cikin adadin 132 yara ne kanana 'yan kasa da 16 ne.

A cewarsa, 'yan bindigar sanye da kayan jami'an tsaro ne suka shiga cikin makarantar sannan suka bude wuta.

Jami'an tsaron Pakistan sun ce suna kokarin kawo karshen fito-na-fito da 'yan bindigar.

Kakakin Taliban na Pakistan ya ce sun dauki matakinne a matsayin mayar da martani kan hare-haren da ake kai wa mayakansu a Arewacin Waziristan da kuma lardin Khyber.

Fira ministan Pakistan, Nawaz Sharif ya yi tur da harin.