Rasha ta kara kudin ruwa

Mutanen Rasha
Image caption Mutanen Rasha

Rasha ta kara yawan kudin ruwa da za a rinka caji a kasar daga kashi goma da digo biyar zuwa kashi 17 bisa dari.

Babban bankin kasar ya ce an yanke shawarar ne domin takaita hauhawar farashin kaya da za a samu da karewar darajar kudin kasar.

Hakan dai ya zo ne 'yan sa'oi bayan darajar kudin kasar ta Rasha watau rouble ta yi faduwar da ba ta taba yin irin ta ba tun a shekarar 1998.

Man fetur da gas ne manyan albarkatun da Rashar take fitarwa zuwa kasashen waje, to kuma faduwar farashin man a duniya ta yi matukar illa ga tattalin arzikin kasar.

Har ila yau kuma takunkumin da kasashen yammacin duniya suka kargamawa kasar ta Rasha saboda zargin hannun ta a rikicin ta Ukraine, shi ma ya yi matukar illa ga tattalin arzikin na Rasha.

Karin bayani