Skype ya kirkiro tsarin fassara harshe

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bambancin harshe ba zai zama matsala ba tsakanin masu amfani da Skype

Kamfanin Microsoft ya kirkiro tsarin fassara hirar da masu amfani da Skype ke yi a harshen Ingilishi da Spaniyanci.

Hakan na nufin yayin hira ko tattaunawa ta bidiyo a Skype, masu magana da wadannan harsuna za su iya fahimtar junansu.

Wannan na nufin an samu cigaba wajen fassara harsuna a tsarin Skype.

Gurdeep Pall na kamfanin Microsoft ya ce an samu wannan nasara ne sakamakon bincike na sama da shekaru 10.

Ya ce wannan nasara za ta bayar da dama mai yawa ga mutane a fadin duniya su rika sada zumunta da tattaunawa tsakaninsu duk da bambancin harshensu.

Jami'in ya kara da cewa daga yanzu yare ko wurin da mutum yake ba za su zama matsala gare shi ba wajen sada zumunta ko magana da wani mutumin a wani wuri.

Hakkin mallakar hoto Reuters

An jarraba wannan tsari a tsakanin 'yan makaranta a Mexico City da Tacoma a Washington, inda 'yan wani aji suke magana da harshen Spaniyanci daya kuma na yi da Ingilishi.

Tsarin na fassara harshen na Skype, yanzu ana da shi ne a harshen Spaniyanci da Ingilishi, amma Microsoft ya ce nan gaba za a samar da na wasu harsuna.

Microsoft ya ce mutane sama da miliyan 300 ne ke amfani da Skype a kowana wata.

Hakan na nufin a duk rana a Skype ana tattaunawa ta sama da minti miliyan dubu biyu.