Blackberry ta koma gidan jiya

Hakkin mallakar hoto Getty

Kamfanin Blackeberry ya kirkiro wata sabuwar waya ta komai da ruwanka ta daban, mai suna Classic.

Wayar tana da madannin lambobi da harufa(keyboard) irin na wayoyin kamfanin na da, da ya sa ta yi fice kafin wayoyin wasu kamfanonin su wuce ta a farin jini.

Bayan madannin na zahiri, Classic din tana kuma da madanni irin na wayoyin zamani na cikin fuska (touchscreen).

Haka kuma tana da kyamara a baya mai karfin megapixel takwas, ga hanzarin kama intanet kamar yadda kamfanin ya bayyana.

Hakkin mallakar hoto Getty

Masu lura da dabarun kasuwanci sun ce kamfanin ya koma tsarinsa ne na da, domin ya farfado da kasuwarsa.

Kuma wasunsu na ganin, da wuya hakan ya jawo hankalin wasu mutanen, ko da ike dai zai iya sa kasuwar wayar ta dore.

Wata mai lura da harkokin kasuwanci, Carolina Milanesi, na ganin wannan dabara ce ta rike mutanen da suke amfani da wayar kamfanin maimakon neman karin wasu sababbi.

Ta kara da cewa tana ganin watakila mutanen da suka saba da wayoyi na zamani masu madanni na cikin fuska(touchscreen) su ga Classic din a matsayin wani abin burgewa, su karbe ta, saboda madannin na zahiri.