'Yan gudun hijira 150 sun kamu da kwalara

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan gudun hijirar na cikin mawuyacin hali

Cutar kwalara ta barke a sansanin 'yan gudun hijira a jamhuriyyar Nijar.

Sansanin wanda ke jihar Diffa yana dauke da dubban 'yan gudun hijira ne daga Najeria wadanda suka gujewa hare-haren 'yan Boko Haram.

Wata majiyar gwamanati ta ce sama da mutane 150 ne suka kamu da cutar, tara daga cikinsu kuma suka mutu.

'Yan gudun hijirar dai na ci gaba da fuskantar mummunan yanayi tun da rikicin na Boko Haram ya raba su da gidajensu